..Imam Ali shine igiyar Allah mai karfi…”
Al-Mirzat Tabriziy ya cigaba har zuwa in da yake cewa:
“Kuma Imam Ali shine irin Manzo,tsaran Annabi (sawa),shine nafsin Manzon Allah (sawa) ,shine idon Allah mai gani,shine hannun Allah shimfidadde,shine kunnen Allah mai ji”
Wannan akan asasin -kaman yanda ka sani ko zaka sani –ka’ida da ta gangaro daga hadisi Qudsi wanda a cikinshi Allah Subhanahu wa Ta’ala yake bayanin waliyyanshi.Mun sha karanta maka wannan hadisin a jalasosi daban daban kuma kai ma ka san shi.Saboda kada kace ya za a yi ya zama hannun Allah?Yaya za a yi ya zama idon Allah?Ya za a yi ?Ya za a yi ?Ya za a yi?
As-Sayyid Kamal Haidariy a littafinshi “Minal Khalqi Ilal Khaiq”,yana cewa dangane da Manzon Allah (sawa) kafin Imam Ali(as),yana cewa:
“Idan muna so mu fadi da wani ibara na ta’abiri daban dangane da Manzon Allah (sawa),shine wasida tsakanin bayi da Allah,tsakanin halittu da Allah a wurin saukowa daga Allah da kuma a wurin komawa ya zuwa gare shi.Kaman yanda Manzon Allah shine wasida a wurin samarwa,samar da halittu a wurin saukowa da cirowa daga Allah,to,haka a wurin komawa,shi Manzon Allah (sawa) shine wasida mafi cika ga isar kowane ma’abucin kamala zuwa ga kamalarshi wadda ake tsammani zuwa cika-Dole sai ta hanyar shi ake saukowa,sai kuma ta hanyar shi ake hawa,domin shine “Al-Haqiqatul Muhammadiyyah” wadda aka yi maka bayanin ta a majaloli daban daban.
“Domin shi Manzon Allah (sawa) ya kai ga mafi kololuwar martaba na takamul da kammala a “qaus” din komawa zuwa ga Allah,a kamaloli,a “sair” da “safar” dinshi a cikin “asma” da “sifat”a taqaice kace.Domin bayan ya kammala wannan tafiyar tashi a cikin sunaye da siffofin Allah an yi mashi rawani da wato an yi mashi kambi,an sa mashi tagiya,an nada mashi maqami madaukaki wanda wani bai kai ya zuwa gare shi ba bayanshi,kuma wani ba zai kai ga zuwa gare shi ba a gabaninshi.
“Ta yadda yake ya daukaka daga makamin “Jam’ul Jam’I”-ba zamu yi bayanin wannan ba saboda mun sha yin bayani.Shine wannan wanda fadin Allah Ta’ala ke ishara zuwa shine “maqamin qaba qausaini”,ya wuce wannan maqamin-zuwa maqamin “Ahadiyyatul Jam’I” wanda yake shine abinda fadin Allah yake ishara zuwa gare shi da “Au adna”.
Ya wuce maqamin “qaba qausaini” ya kai “adna”.
“Saboda haka sai ya kebanta Sallallahu Alaihi wa Alihi da wannan maqamin na “au adna” ta fuskacin asala da kebanta ta zati.Su kuma mutanen gidanshi sai ya zama sun daukaka ya zuwa ga wannan matsayin na “adna” ta hanyar gado daga gare shi Afdalu Salawatul Musallin.
Saboda haka sai ya zama sune jin Allah,ganin Allah ila akhiri da sauransu da sauransu.Saboda suna a mafi daukaka a cikin Auliyyah da “mazhahir” na “tajalliyat”din siffofi da sunaye na Allah Subhanahu wa Ta’ala kaman yanda ya bayyana a mahallinshi.
Sai As-Sayyid Haidariy ya cigaba da cewa:
“Ya za a yi Manzon Allah Sallallahu alaihi wa Alihi wasallam matsayinshi ba zai iya daukaka ba?Saboda haka ya zama shine mafi kusa da Allah banda sauran abinda suke cikin duniya din …ilah akhirihi ila akhirihi…
Saboda haka Imam Ali,lokacin da ake cewa shine kaza,shine kaza,dubi ya zuwa ga wannan hadisin Qudsi inda Manzon Allah (sawa),inda Allah yake cewa:
“MA YAZALU ABDIY YATAQARRABU ILAYYA BIL FARADI HATTA UHIBBAHU,FA IZA AHBABTUHU SARA SAM’I ……ila akhirihi”
Ma’ana; Bawa na ba ya gushewa yana kusanta ya zuwa gare ni ta hanyar fara’id har ya zama na so shi,na kauna ce shi.To,in na kaunace shi sai ya zama shine jina ……Wannan shine “Qurbul Fara’id”
Sannan akwai wani kusanci day a zo a hadisi daban in da yake cewa:
“Bawa ba ya gushewa yana kusanto wa ya zuwa gare ni da nawafil har ya zama cewa ina sonshi,to,in ya zama haka,sai in kasance jinshi da ganinshi da sauransu …ila akhirihi”
Akan asasin wannan hadisin ne muka tsamo wa’yannan ababen da muke fadi kaman yanda Al-Mirzat Tabriziy ya ambata inda yake cewa Imam Ali (as) shine idon Allah.Shima kanshi Imam Ali(as) ya fadi wannan inda yake cewa:
“ANA JAMBULLAH ALLAZIY FARRADTUM” Wato nine Jambullah wanda kuka yi tafridi a cikinshi.Da zaku je kuyi nadama ranar Alkiyama “YA HASRATA ALA MA FARRADTU…zuwa karshen ayan”
To,sai Al-Mirzat Tabriziy ya cigaba da cewa:
“…Shine jambullah,Sannan shine hannun Allah,Shine idonshi da kunnuwanshi da sauransu.Shine wanda aka kare daga zamiya,shine wanda aka tsarkake shi daga rashin tawazun da “idrad”,shine wanda aka tsarakake daga aibu wato bai da naqas,wanda aka tsarkake shi daga shakka,dan uwan Annabi,wasiyyin Annabi,wannan mai kwana akan shimfidanshi(sawa) a ranar hijra,shine wannan wanda yake yaye bakin ciki daga fuskan Annabi (sawa),wannan wanda Allah Subhanahu wa Ta’ala ya sanya shi takobi ga Annabcin Annabi(sawa),ya sanya shi ya zama aya da hujja akan gasgatawan gaskiyan sakon Annabi.
Kaman yanda Ayatullah As-Sayyidul Khu’I yake fadi,yana cewa samuwar Imam Ali (as) a cikin Sahabban Annabi dalili ne akan ingancin Annabi din.Wato,babu wanda zai iya sana’anta Ali saidai in Annabi,Annabin ma sai ya kasance khatimul Anbiyya.Babu wanda zai iya sana’anta Ali sai irin Annabi (sawa) don ba mutum bane “adi”.
“..Shi (Imam Ali) hujja ne akan ingancin sakon Annabi(sawa),shi Allah Ta’ala ya sanya shi mai sheda ne akan al’ummar Annabi,Allah ya sanya shi madaukin tutar Annabi-wadannan dukkansu isharori ne masu yawa masu yalwa –Allah Ya sanya shi kariya ga manhajin Annabi,WA YADAN LI BU’USIHI ….ila akhiri ila akhirihi.”
Har inda yake cewa:
“Kuma shine sunan Allah mafi girma,shine Al-Kur’ani mafi karimci,shine daki mai alfarma,shine Safa,shine Marwa ,shine Zamzam,shine mazhari na ababen mamaki,shine mazhari na bakin abubuwa,shine tauraruwa wadda Allah yake amfani da ita domin ya jefi shedanu da ita (shooting star),shine mai tarwatsa rundununonin mayaka,shine markazi na da’irar dukkan bukatu(wato mai amsa bugatun bayin Allah),shine mahaifin A’immah,shine mai raya sunnah,mai yaye bakin cikin al’umma,shine shugaban al’umma,shine ma’abucin zabi-wato,shine wanda Allah Ta’ala ya zaba(Al-Mujtaba).
“…shine wanda aka kebe domin ‘yan uwantaka da Manzon Allah(sawa),shine na biyar daga cikin mazowa mayafi,shine mai rikon tuta,shine wannan digon a karkashin “b” ta “Bismillahir Rahmanir Rahim”,shine abokin Annabawa,shine malamin Jibril,sarkin Mika’il,shine hakimin Izra’il,shine mai raba aljanna da wuta,shine mahaifin Shubbar da Shubair(wato Hasan da Husain),shine shugaban ‘yan Adam,duk wanda ya ki haka,hakika ya kafirta.
Saboda ya zo cikin Amaaliy na Ash-Shaikhus Saduq da isnadinshi zuwa ga Huzaifa daga Annabi(sawa) cewa:
“ALIYUB NU ABI TALIB KHAIRUL BASHAR,WA MAN ABA FAQAD KAFAR”
Ma’ana;Ali dan Abi Talib shine mafi alherin ‘yan Adam,wanda ya ki,hakika ya kafirta.Kuma ya rawaito irin shi daga Jabir Ibn Abdullahil Ansariy ….ila akhiri.
“…WA HUWA MALAZUL LA’IZIN ,WA GIYASUL MUDDARRIN,WA HAKIMU YAUMAD DIN,WA HABIBU ILAHIL ALAAMIN,WA HUJJATILLAHI ALAL AWWALINA WAL AKHIRIN,WA HAYATUL ALAMIN,WA HUWA SIRRUL ASRAR,WA NURUL ANWAR,WA IMAMUL ADHAR,WA WALIYYUL JABBAR,NI’IMATULLAHI ALAL ABRAR,WA NIQMATUHU ALAL FUJJAR..
Ya cigaba da cewa:
“..WA HUWA HABIBULLAHIL ALIY,WA WAJHUHUL MADIY,WA NAFSUHUL WAFIY,AL-IMAMU ABUL HASANI ALI…”
Da sauran siffofi da fada’il wa’yanda ya ambata dangane da Ali(as),da haihuwan shi a 13 ga watan Rajab wa’yanda bamu da lokacin ko karanta ma balle yin bayanin su,wannan yasa muka tuna da shi’iri wanda baiti mun sha fadi a wurare in da wani ya rera mashi(Imam Ali) cewa:
“WA QALU ALIYUN ALA,FA QULTU LA,FA INNAL ULA BI ALIYIN ALA”
Ma’ana;Kuma sunce wai Ali ya daukaka,ni ko nace a’a,domin ita daukakar da Ali ne ta daukaka.
Wannan abinda muke fadi darajoji da ya same su,ya same su ne albarkar tarbiyya da bibiya da kuma gado “ma’anawiy badiniy haqiqiy” daga Manzon Allah (sawa).Manzon Allah (sawa) shi ya raine shi(Imam Ali),da hukuncin Allah ya dauko shi daga wurin mahaifinshi Abu Talib tun yana dan karamin yaro.Ya killace shi domin kanshi –kowa ya san wannan.
Akwai cigaba.288
29 Mayu 2017 - 10:02
Lambar labari: 832707
Na Maulana Sheikh Hamzah Muhammad Lawal(ama) Yusuf Sulaiman ya rubuta maku …Cigaba